Za a sayar da Swansea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan Swansea, Francesco Guidolin

Kulob ɗin Swansea City ya ba da tabbacin fara tattaunawa da masu 'yan kasuwar Amurka, Jason Levien da Steve Kaplan wajen sanya hannun jari a kulob ɗin.

Magoya bayan ƙungiyar wasan suna son a cimma yarjejeniyar a 'yan makonni masu zuwa.

Ana sa ran yarjejeniyar wadda za ta kama a kan kuɗi Fam miliyan 100, za ta ba wa shugabanni kulob damar ci gaba da riƙe kaso 21 na hannun jarin ƙungiyar.

A 2011 ne Swansea ta samu damar cancanta buga wasannin gasar Premier Ingila.