An ci kwallaye 217 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption An buga wasannin mako na 11 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Kwallaye 217 aka zazzaga a raga a wasanni 101 da aka yi a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria, bayan da aka kammala wasannin mako na 11.

A karshen makon nan ne aka buga wasanni 9 a gasar aka ci kwallaye 16, kungiyoyin da suka buga wasa a gida su 8 suka cinye wasanninsu aka yi canjaras a karawa daya kacal.

'Yan wasa uku ne ke kan gaba a yawan zura kwallaye a raga a gasar da suka hada da Okpotu na Lobi Stars da Egbuchulam na Rangers da kuma dan wasan El-Kanemi Warriors Mustapha wanda kowannensu ya ci 6.

Wadanda suka ci kwallaye biyar - biyar a gasar sun hada da Jimoh na 3SC da Obaje na Wikki Tourists da kuma dan kwallon Niger Tornadoes Gata.