Rooney zai iya buga wasan da Man U za ta yi da West Ham

Hakkin mallakar hoto Reuters

zai yi buga a wasan kofin FA da kulob din Manchester United zai yi da West Ham a ranar Laraba bayan ya dawo daga wasan 'yan kasa da shekara 21.

A yayin da koci Louis van Gaal ya ke kallo, kaftin din Ingilan ya bugawa kulob din matasan tsawon mintuna 61 a karawarsu da Middlesbrough a ranar Litinin.

Dan wasan ya rasa wasanni 12 tunda ya ji rauni a gwiwarsa a gasar kofin firimiya da Sunderland ta yi nasara a ranar 13 ga watan Faburairu.

Van Gaal ya ce Rooney -- mai shekara 30 -- zai iya wasa a gasar idan ya tabbatar cewa zai iya.