Super Falcons za ta kara da Senegal

Hakkin mallakar hoto Thenff twitter
Image caption A wasan farko da suka yi a Senegal tashi suka yi 1-1

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Super Falcons za ta kara da ta Senegal a wasa na biyu a neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka ta mata.

A wasan farko da kasashen biyu suka fafata a Senegal a ranar 8 ga watan Afirilu, tashi suka yi kunnen doki 1-1.

Duk tawagar da ta yi nasara, za ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da Kamaru za ta karbi bakuncin gasa ta 10 da za a yi a bana.

Nigeria ce ke rike da kofin nahiyar Afirka a kwallon kafar mata da ta lashe a 2014 , kuma kofi na 10 da ta dauka jumulla.