EURO 2016: Faransa ba za ta gayyaci Benzema ba

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Karim Benzema mai taka leda a Real Madrid ta Spain

Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta yanke cewar Karim Benzema ba zai wakilceta a gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a bana ba.

Ana binciken Benzema, mai taka leda a Real Madrid da zargin sa hannu kan batawa abokin wasansa suna Mathieu Valbuena.

A cikin watan Disamba aka dakatar da Benzema daga buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa wasanni.

Dan wasan wanda ya karyata aikata ba daidai ba, ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na Twitter cewar hukuncin abin takaicine ga kansa da magoya bayansa.

Faransa ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai da za a fara ranar 10 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan Yulin shekaran nan.