An cire Djokovic daga gasar Monte Carlo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amn fitar da Djokovic daga gasar Monte Carlo ta kwararru

Jiri Vesely ya fitar da zakaran wasan kwallon tennis na duniya, Novak Djokovic daga gasar kwararru da ake yi a Monte Carlo.

Vesely wanda yake mataki na 55 a jerin wadanda suka fi iya wasan kwallon tennis a duniya ya doke Djokovic ne da ci 6-4 2-6 6-4.

Wannan ne kuma karon farko da aka fitar da Djokovic a zagayen farko na wata gasa tun bayan da aka yi waje da shi a gasar kwararru ta Madrid a shekarar 2013.

Djokovic ya lashe wasanni 22 daga cikin gasar kwararru tara dada cikin goma da ya fafata.