Zaben gwarzon 'yan wasan Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester ce ke matsayi na daya a kan teburin Premier

'Yan wasan Leicester uku suna daga cikin guda shida da za a zabi gwarzon dan wasan da ya fi yin fice a gasar Premier ta bana.

'Yan wasan uku na Leicester sun hada da Jamie Vardy da Riyad Mahrez da kuma N'Golo Kante.

Sauran ukun da suke cikin takara sun hada da Mesut Ozil na Arsenal da dan wasan West Ham Dimitri Payet da kuma dan kwallon Tottenham Harry Kane.

Haka kuma Kane din dai yana cikin jerin sunayen 'yan takara da za a fitar da matashin dan wasa da ya fi yin fice a gasar wanda ya lashe a bara.

Zai kuma yi takarar ne har da abokin taka ledarsa a Tottenham, Dele Ali.

Za a bayyana 'yan wasan da suka yi fice a gasar ta Premier a ranar Lahadi 24 ga watan Afirilu.

'Yan wasan da za a zabi gwarzon Premier

Dimitri Payet (West Ham)

Harry Kane (Tottenham)

Jamie Vardy (Leicester)

Mesut Ozil (Arsenal)

N'Golo Kante (Leicester)

Riyad Mahrez (Leicester)

Matasan 'yan wasa

Dele Alli (Tottenham)

Harry Kane (Tottenham)

Jack Butland (Stoke)

Philippe Coutinho (Liverpool)

Romelu Lukaku (Everton)

Ross Barkley (Everton)

Macen da ta fi kwazo a Premier

Beth Mead (Sunderland)

Gemma Davison (Chelsea)

Hedvig Lindahl (Chelsea)

Izzy Christiansen (Manchester City)

Ji So-Yun (Chelsea)

Matashiyar da ta fi yin fice

Beth Mead (Sunderland)

Danielle Carter (Arsenal)

Hannah Blundell (Chelsea)

Keira Walsh (Manchester City)

Nikita Parris (Manchester City)