Cristiano Ronaldo ya yabi kansa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Cristiano Ronaldo ya mayar wa masu suka martani bayan kwallaye ukun da ya ci wa Real Madrid wanda ya kai kungiyar ga samun nasarar zuwa wasan daf da na karshe a gasar zakarun Turai.

A wasan da a ka buga ranar Talata Real ta fanshe cin da Wolfsburg ta yi mata na 2-0 a karawarsu ta farko inda a yanzu haka, sakamakon wasan ya zama ci 3-2.

A watan Faburairu ne dan wasan gaban na Portugal ya fice daga wajen wani taron manema labarai bayan an tambaye shi nasarorin da ya samu a wasannin da ya buga na wannan kakar wasan.

Ronaldo ya ce, "A baya sai na ga kamar wannan kakar wasan bata karbe ni ba, amma kuma babu laifi."