Ana binciken asusun tallafin Drogba

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Drogba ya ci kwallaye 164 a lokacinsa biyu a Chelsea

Hukumar kula da bayar da tallafi ta Ingila tana binciken asusun tallafi na Didier Drogba bisa abin da ta kira manyan abubuwan saba kai'da.

Jaridar Daily Mail ta yi ikirarin cewa fan 14, 115 kawai daga cikin fam miliyan daya da dubu 700 da aka bayar gudummawa ga asusun tallafin na Drogba aka yi amfani da su domin taimako a Afrika.

Tsohon dan wasan na Chelsea mai shekara 38, na barazanar daukar matakin shari'a a kan lamarin inda ya bayyana labarin jaridar ta Mail a matsayin karyda da kuma bata suna.

A wata sanarwa da ya fitar, dan wasan dan Ivory Coast ya kara da cewa, ''ba zamba ba almundahana ba almubazzaranci ba kuma karya''.

Drogba wanda ke wasa a kungiyar Montreal Impact ta Canada ya zargi 'yan jaridar ta Mail da jefa rayuwar dubban yaran Afrika cikin hadari.

A 2009 aka kaddamar da asusun tallafin na Drogba a Biritaniya, lokacin tsohon kyaftin din na Ivory Coast yana wasa a Chelsea.

A rubutun da ta yi jaridar ta Mail ta yi ikirarin cewa an kashe fan 439,321 a tarukan liyafar tara kudi da manya da wasu fitattun jama'a ke halarta, yayin da kuma sama da fan miliyan daya ke ajiye kawai a bankuna.

Sai dai hukumar asusun ta sheda wa jaridar cewa tana da wata kungiyar daban mai irin wannan suna da aka kafa a Ivory Coast, wadda ta samar da kudi wurin gudanar da ayyukan jin kai da dama a Afrika tun 2007.

A sanarwar tasa Drogba ya zayyana ayyukan da asusun nasa ya yi da suka hada da, samar da asusun tafi-da-gidanka, da kafa gidan kula da marayu da sayen na'urar wankin koda ta masu ciwon koda da sayen jakunkunan makaranta da littattafai ga dalibai.

Dan wasan ya kara da cewa, ''iyayena talakawa ne kuma na yi aiki ne tukuru kafin na zama abin da na zama a yau, amma hakan ba zai amfane ni da komai ba idan ban taimaki kasata da nahiyata da kuma al'ummata ba''.