Gutierrez ya yi nasara a kotu kan Newscastle

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A yanzu Jonas Gutierrez yana Deportivo La Coruna

Tsohon dan wasan Newcastle Jonas Gutierrez ya yi nasara a karar da ya shigar da Newcastle United kan nuna masa wariya.

Dan wasan ya bar Newcastle United a watan Mayu na 2015 bayan zamansa a kungiyar na shekara bakwai.

Wata kotun kwadago ta gano cewa kungiyar ta ajiye dan wasan na tsakiya ne saboda likitoci sun gano yana dauke da cutar daji.

Gutierrez mai shekara 32 ya shigar da karar ne inda ya nemi diyyar fam miliyan biyu bisa nuna masa wariya saboda larurar lafiya.

A nan gaba ne kuma kotun za ta sake zama inda za ta duba batun biyansa wata diyyar ta daban.

A watan Oktoba na 2013 ne aka gano cewa Gutierrez wanda ya koma New Castle daga Real Mallorca a 2008 yana dauke da cutar daji ta marena.

Kafin a gano yana da cutar yana yi wa kungiyar wasa akai akai inda ya ci kwallo goma a wasanni 177.

Dan wasan wanda ke buga wa kungiyar kasa ta Argentina ya shigar da Newcastle kara saboda abin da kungiyar ta yi masa bayan da aka gano yana da cutar, yana mai cewa kungiyar ta Premier ta dauke shi a matsayin wani jidali bayan da ya dawo daga magani.