Europa: Liverpool ta doke Dortmund 5-4

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool ta tsallake rijiya da baya

Liverpool ta kai wasan kusa da karshe a gasar kofin Zakarun Turai na Europa bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 5-4 jumulla, wasa gida da waje.

A wasan na ranar Alhamis wanda aka yi a Ingila shi ne karo na biyu, sun tashi Liverpool na da ci 4-3, bayan da a haduwarsu ta farko a Jamus suka yi kunnen doki 1-1.

Da wannan sakamako Liverpool ta kai wasan kusa da karshe kenan da jumullar kwallaye 5-4.

A sauran wasannin da aka yi na karon na biyu na matakin dab da na kusa da karshen a daren na Alhamis, Shaktar Donetsk ta ci Sporting Braga 4-0.

A haduwarsu ta farko Shaktar Donetsk din ce dai ta ci Sporting Braga 2-1, hakan ya sa ta kai wasan kusa da karshe da kwallaye 6-1.

Sparta Praha wadda ke gida ta sha kashi a hannun Villareal da ci 4-2, bayan da a karawar farko Villareal din ta ci 2-1, hakan ya sa ta tsallake ita ma da ci 6-3.

Sevilla wadda ta ci Athletic Club 2-1 a karawarsu ta farko, ta karbi bakuncin Athletic din wadda ita ma ta ci ta 2-1, har suka kai bugun fanareti bayan karin lokaci, inda a karshe Sevilla ta yi nasara da ci 5-4 a fanareti, jumullar kwallaye kuwa ta yi galaba da ci 7-6.

A ranar Juma'a ne za a fitar da jadawalin wasan kusa da karshe na gasar kofin Europan da kuma na Zakarun Turai.

A jadawalin da za a fitar Manchester City za ta san wadda za ta kara da ita tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid da kuma Bayern Munich.