Europa: Liverpool za ta kara da Villarreal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Alhamis ne Liverpool ta samu nasara kan Borussia Dortmund

Kungiyar Liverpool za ta fafata da Villarreal a wasan daf da na karshe na gasar Europa.

Nasarar da Liverpool ta yi ranar Alhamis a kan Borussia Dortmund ce ta zama silar zuwa Sipaniya ranar 28 ga watan Afrilu don karawar farko, sannan kuma su sake karawa a Anfield ranar 5 ga watan Mayu.

Ita kuwa Sevilla za ta kara ne da kungiyar Shakhtar Donetsk, ta kasar Ukraine su ma a wasan daf da na karshe din.

Za a yi wasan karshe na gasar ne a Basel da ke Switzerland, ranar 18 ga watan Mayu.