Schweinsteiger ya gama buga wasannin bana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Van Gaal ya ce mai yiwuwa dan wasan ya wartsake zuwa kakar badi

Kociyan Manchester United Louis van Gaal, ya ce zai yi wahala dan wasan tsakiya na kungiyar Bastian Schweinsteiger, ya sake buga wa kulob din wasa a bana.

Schweinsteiger dan shekara 31 yana ta ririta rauni da ya ji ne tun lokacin da yake Bayern Munich a watan Yulin bara.

Van Gaal ya ce, "Mai yiwuwa ya wartsake zuwa kakar wasan badi."

Schweinsteiger ya buga wa Manchester United wasanni 31 tun komawarsa kungiyar.

Sai dai ana ganin Schweinsteiger zai iya bugawa Jamus wasa a gasar Euro 2016 da za a yi a Faransa a wannan bazarar.