Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa nan domin sabunta shafin

Hakkin mallakar hoto Getty

Barkanmu da ziyarta shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa a Asabar musamman irin wainar da ake toyawa a nahiyar Turai dama duniya.

4:15 Manchester City za ta kara da Real Madrid a wasan daf da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan na nufin cewa City za ta iya fuskanci sabon kocinta mai jiran gado Pep Guardiola, a wasan karshe.

Guardiola zai maye gurbin tsohon kociyan City Manuel Pelligrini a lokacin bazara.

Za a yi wasan zagaye na farko a filin wasa na Etihad da ke Manchester ranar 26 ga watan Afrilu, a kuma yi zagaye na biyu a babban birnin Sipaniya ranar 4 ga watan Mayu.

3:21 Bayan da aka shiga mako na 12 a gasar Firimiyar Nigeria ga yadda teburi yake na 10 farko a gasar.

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter

1:52 Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Musa Hamisu Ali: Aston Villa yau fa sai kun yi da gaske, domin kuwa idan ku ka yi sakaci Manchester United za su yi muku ruwan kwallaye, mu kuma ga shi bama so suje Champions league.

Bashar Kansila Maitukunya Dirin Daji Jahar Kebbi: Tabbas alamar karfi tana ga mai kiba, ko shakka babu Man United ita za ta yi nasara a wannan wasa tsakanin ta da Aston Villa da ci 4 da nema..Up Rashford

Jameelou Badamasi Batsari: Duk da Aston Villa tafi kowa zama koma baya a wannan kakar wasan. Muna fatan za ta lallasa Manchaster Unated daci uku da nema. UpArsenal

Muttawakkil Gambo Doko: Yan Man United wannan wasan fa sai kunyi da gaske idan ba hakaba za ku ga raina kama kaga gayya.

Umar Alassan Kamaru: A gaskiya wannan wasan zai mutukar daukar hankalin yan kallo amma ina tunanin Manchester United za ta lallasa Aston Villa da ci uku da nema.

1:40 'Yan damben Ebola da Mai Takwasara da suke tashe a wasan damben gargajiya a yanzu.

'Yan wasan biyu sun kara a cikin watan Fabrairu a Zaria, Jihar Kaduna, inda Ebola ya kashe Mai Takwasara a turmi na biyu, sun kuma kara a jihar Sokoto a cikin watan Afirilu suka tashi wasa babu kisa. Ana sa ran za su sake fafatawa a jihar Kano daga tsakanin Juma'a 22 zuwa 24 ga watan Afirilu, domin fitar da gwanin dambe a tsakaninsu.

1:32 Jamie Murray da kuma Bruno Soares sun kai wasan karshe a gasar kwallon tennis ta 'yan wasa biyu da ake yi a Monte Carlo.

Hakkin mallakar hoto Getty

'Yan wasan wadanda suka lashe kofin Australian Open sun casa Marcelo Melo da ci Ivan Dodig da ci 6-2 6-4 a cikin minti 67 da suka fafata a tsakaninsu.

1:24 Lewis Hamilton zai fara gasar tseren motoci ta Chinese Grand Prix a mataki na karshe a gasar da za a yi.

Abokin tserensa Nico Rosberg mai tuka motar Mercedes shi ne ke kan layi a matsayi na daya, sai Daniel Ricciardo matukin motar Red Bull a matsayi na biyu, da kuma Kimi Raikkonen mai tuka motar Ferrari na uku a jerin fara tsere.

Hamilton matukin motar Mercedes ya ci karo da cikas din da ya sa abokin wasansa Nico Rosberg ya ba shi tazarar maki 17.

1:10 Gasar Firmiyar Nigeria wasannin mako na 12

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
 • Shooting Stars vs Heartland
 • Nasarawa United vs Plateau United

1:00 Za a buga gasar cin kofin Ghana a wasan kwallon kafa ta mata, wadda za a yi siri daya kwale. Tuni aka raba kungiyoyin zuwa shiyya biyu.

Hakkin mallakar hoto Ghanafa Twitter

Shiyyar Arewacin kasar:

 • Ampem Darkoa Ladies
 • Prisons Ladies
 • Fabulous Ladies
 • Ashtown Ladies
 • Lepo Ladies
 • Real Upper Northern
 • Subayo Golden Ladies

Shiyyar Kudanci:

 • Hasaacas Lady
 • Bafana Ladies
 • Soccer Intellectuals
 • Halifax Ladies
 • Police
 • Samaria Ladies
 • Immigration Ladies
 • Lady Strikers

12:26 An ci kwallaye 226 a wasanni 105 da aka buga a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria, kuma an shiga mako na 12.

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter

'Yan wasa shida ne suka ci kwallaye shida-shida a gasar ta Firimiyar Nigeria

12:20 Gasar Holland mako na 31

5:30 Vitesse Arnhem vs Heracles Almelo

6:45 Feyenoord Rotterdam vs FC Groningen

6:45 AZ Alkmaar vs PEC Zwolle

7:45 Roda JC Kerkrade vs PSV Eindhoven

12:15 Gasar Jamus Bundesliga mako na 30

 • 2:30 SV Werder Bremen vs VfL Wolfsburg
 • 2:30 Bayer 04 Leverkusen vs Eintracht Frankfurt
 • 2:30 FC Augsburg vs VfB Stuttgart
 • 2:30 TSG Hoffenheim vs Hertha Berlin
 • 2:30 Darmstadt vs FC Ingolstadt 04
 • 5:30 Bayern Munich vs Schalke 04

Gasar Faransa League 1 mako na 34

 • 4:00 Paris Saint-Germain vs Caen
 • 7:00 Lorient vs Toulouse FC
 • 7:00 FC Girondins de Bordeaux vs Angers
 • 7:00 ES Troyes AC vs Stade de Reims
 • 7:00 GFC Ajaccio vs Lille OSC
 • 7:00 Bastia vs Saint Etienne
Hakkin mallakar hoto Getty

12:10 Gasar Spanish Laliga mako na 33

 • 3:00 Getafe CF vs Real Madrid CF
 • 5:15 Las Palmas vs Sporting Gijon
 • 7:30 SD Eibar vs Real Sociedad
 • 9:05 Celta de Vigo vs Real Betis

Gasar Italian Serie A mako na 33

 • 2:00 Bologna FC vs Torino FC
 • 5:00 Carpi vs Genoa CFC
 • 7:45 Internazionale vs Napoli

12:05 A shirinmu na sharhi da bayanai a gasar cin kofin Premier,

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan makon za mu kawo muku gasar sati na 34 ne a karawar da za a yi tsakanin Manchester United da Aston Villa. Za mu fara gabatar da shirin da karfe 2:30 agogon Nigeria da Nijar. Za kuma ku iya bayar da gudun mawarku a lokacin da ake gabatar da shirin a dandalinmu na muhawara da sada zumunta a BBC Hausa Facebook da kuma Google +.

12:00 Gasar English Premier League mako na 34

 • 12:45 Norwich City vs Sunderland
 • 3:00 Everton FC vs Southampton FC
 • 3:00 Manchester United vs Aston Villa
 • 3:00 Newcastle United FC vs Swansea
 • 3:00 West Bromwich Albion FC vs Watford
 • 5:30 Chelsea FC vs Manchester City