Man United ta samu nasara a kan Villa

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Kwallo ta hudu da Rashford ya ci wa United a Premier

Manchester United ta doke Aston Villa da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 34 da suka fafata a Old Trafford a ranar Asabar.

Marcus Rashford ne ya ci kwallon kuma ta hudu da ya ci a gasar ta Premier, kuma ta bakwai da ya ci wa United a wasanni 12 da ya buga mata a bana.

Hakan ne ya sa ya kafa tarihin matashin dan wasan United da ya ci kwallaye hudu a gasar ta Premier bai kai shekara 19 da haihuwa ba.

Da wannan sakamakon Aston Villa ba za ta buga gasar Premier ta badi ba, kuma karo na tara kenan ta yi rashin nasara a gasar ta Premier a jere.

Ita kuwa United za ta buga wasan mako na gaba a gasar da Crystal Palace.