Olympics: An raba jadawalin wasan kwallon kafa

Hakkin mallakar hoto TheNFF twitter
Image caption Tawagar ta Nigeria tana rukuni na biyu a gasar kwallon kafa da za a yi a Brazil

Tawagar kwallon fa ta Nigeria ta matasa 'yan kasa da shekara 23 za ta fafata da ta Sweden da ta Colombia da kuma ta Japan a gasar kwallon kafa da za a yi a wasannin Olympics.

Nigeria wadda ta taba lashe lambar zinariya a shekarar 1996 a wasan kwallon kafa a gasar ta Olympics tana cikin rukuni na biyu.

Rukunin farko ya kunshi Brazil da Afirka ta Kudu da Denmak da kuma Iraqi.

Fiji da Denmark da Jamus da kuma Jamhuriyar Korea suna cikin rukuni na uku.

Sai kuma rukuni na hudu da ya kunshi Honduras da Algeria da Portugal da kuma Argentina.

Brazil ce za ta karbi bakuncin wasannin Olympics da za a yi a cikin shekarar nan.