Real Madrid ta lallasa Getafe da ci 5-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid tana da maki 75 daga wasanni 33 da ta buga a La Liga

Real Madrid ta samu nasara a kan Getafe da ci 5-1 a gasar La Liga wasan mako na 33 da suka fafata a ranar Asabar.

Madrid ta ci kwallon farko ta hannun Benzema sannan Isco ya kara ta biyu saura minti biyar a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutun Gareth Bale ya ci kwallo na uku, Rodríguez ya ci na hudu, sannan Ronaldo ya kara ta biyar a raga.

Sarabia ne ya ci wa Getafe kwallo daya tilo a raga saura minti takwas a tashi daga wasan.

Da wannan nasarar da Real Madrid ta samu ya sa tana da maki 75, za kuma ta buga wasan mako na 34 ne da Villareal ranar Laraba 20 ga watan Afirilu.

Barcelona wadda ke mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 76, za ta karbi bakuncin Valencia a ranar Lahadi.