Arsenal ta tashi wasa 1-1 da Crystal Palace

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Arsenal ta koma mataki na hudu a kan teburin Premier

Arsenal ta raba maki daya da daya da Crystal Palace, bayan da suka tashi wasa kunnen doki a wasan Premier gasar mako na 34 da suka yi a Emirates.

Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Sanchez daf da za a ta fi hutun rabin lokaci.

Crystal Palace ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Bolasie saura minti tara a tashi daga fafatawar.

Arsenal ta koma mataki na hudu a kan teburin Premier da maki 60, za kuma ta buga wasa na mako na 35 da West Brom a Emirates.

Ita kuwa Crystal Palace tana da maki 39 a matsayi na 16, za kuma ta ziyarci Manchester United a wasan da za ta buga na gaba a gasar ta Premier.