Valencia ta ci Barcelona a Nou Camp

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An fitar da Barcelona daga gasar cin kofin zakarun Turai

Valencia ta doke Barcelona da ci 2-1 a gasar La Liga wasan mako na 33 da suka kara a jiya Lahadi.

Barcelona ce ta fara cin gida ta hannun Ivan Rakitic a minti na 26 da fara wasan, sannan Santiago Mina ya ci wa Valencia ta biyu.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Barcelona ta ci kwallo ta hannun Lionel Messi.

Barcelona da Atletico Madrid suna da maki 76, yayin da Real Madrid ke da maki 75, sai Villareal da maki 60.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka buga:
  • Malaga CF 0 : 1 Athletic de Bilbao
  • Sevilla FC 1 : 1 Deportivo La Coruna
  • Rayo Vallecano 2 : 1 Villarreal CF
  • Atletico Madrid 3 : 0 Granada CF