Shagon Mada da na Alhazai sun yi Canjaras

Image caption Turmi uku suka dambata babu kisa a wannan wasan

An ci gaba da yin gumurzu a damben gargajiya a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei dake Abuja a Nigeria da safiyar Lahadi.

Cikin wasannin da aka yi har da wanda Shagon Mada daga Kudu da Shagon Alhazai Mai kura daga Arewa suka dambata.

Turmi uku suka yi babu kisa, kuma wasan ya kayatar, Alkalin wasa Tirabula ya raba karawar ganin babu wanda ya je kasa a tsakaninsu.

An kuma sa zara tsakanin Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da Bahagon Audu Argungu, kuma turmi biyu suka yi babu kisa aka raba su.

Shi ma wasa tsakanin Nura Dogon Sani daga Arewa da Dan Shaddadu daga Kudu turmi biyun suka taka, kuma karawar ta su ba ta yi kisa ba.

Daga karshe ne aka rufe filin da fafatawa tsakanin Yahaya Kwantagora daga Arewa da Dan Jimama daga Kudu, turmi daya kacal suka yi alkalin wasa ya raba su.