Leicester da West Ham sun buga 2-2

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Leonardo Ullo ne ya farkewa Leicester kwallo ta biyu

Leicester City da West Ham United sun tashi wasa 2-2 a gasar Premier wasan mako na 34 da suka fafata a King Power.

Leicester ce ta fara cin kwallo ta hannun Vardy a minti na 18 da fara tamaula, kuma kwallo ta 22 da ya ci kenan a gasar ta bana.

Bayan da aka dawo ne Andy Carroll ya farkewa West Ham kwallon da aka zura mata a bugun fenariti, sannan Cresswell ya kara ta biyu a ragar Leicester.

Sai dai kuma daf da za a tashi daga karawar Leicester ta samu fenariti kuma Ulloa ya buga ya kuma ci kwallon.

Leicester City ta kammala karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili bayan da aka kori Jarmy Vardy daga wasan bayan da aka dawo daga hutu.

Leicester za ta buga wasan mako na 35 ne a gida da Swansea, yayin da West Ham United za ta karbi bakuncin Watford a wasan gaba da za ta fafata a gasar.