Sunshine Stars ta doke El-Kanemi 3-0

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Kwallaye 15 aka ci a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 12

El-Kanemi Warriors ta yi rashin nasara a hannun Sunshine Stars da ci 3-0 a gasar Firimiyar Nigeria wasannin mako na 12 da suka kara.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi Rivers United daya mai ban haushi ta ci Kano Pillars.

Haka ma Ifeanyi Ubah ta doke Warri Wolves da ci 1-0, ita ma Lobi Stars ta ci Akwa United da ci daya da nema.

Fafatawa tsakanin Giwa FC da Heartland ta shi wasan aka yi saura minti 16 lokaci ya cika, sakamakon hatsaniya da ta barke a wasan, kuma Heartland ta ci kwallo daya.