CAF: Za a buga gasar zakaru a tsakiyar mako

Hakkin mallakar hoto caf
Image caption A karon farko CAF za ta buga wasannin zakarun nahiyar a tsakaiyar mako

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta tsara buga wasannin cin kofin zakarun nahiyar ta bana a tsakiyar mako, kuma a karon farko.

Tun farko an yi ta kiraye-kirayen cewar hukumar da ta dunga yin wasu wasannin a tsakiyar mako maimakon yin su a karshen sati kamar yadda ta saba.

Hakan ne ya sa hukumar ta ce za ta buga wasannin gasar cin kofin zakarun Afirka ta Champions League da kuma ta Confederation a ranar Talata da Laraba.

CAF ta ce hakan zai bai wa kungiyoyin nahiyar da suke buga gasar yin wasannin kasashensu da ake yi a duk mako.

Ga jerin wasannin kofin zakarun Afirka da za a buga a Talata 19 ga watan Afirilu.

CAF Champions League
  • ZESCO United da Stade Malien de Bamako
  • Al-Ahli Tripoli da ASEC Mimosas
  • MO Bejaia da Al Zamalek
  • Entente Sportive da El Merreikh
African Confederation Cup
  • Stade Gabesien da Zanaco
  • G.D. Sagrada Esperan├ža da Vita Club De Mokanda
  • Misr Almaqasa da CS Constantine
  • ES Tunis da Azzam United