An tuhumi Vardy da nuna rashin da'a

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Yadda Vardy ya dunga fadar kalamai ga alakalin wasa Moss

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi dan wasan Leicester City, Jamie Vardy, da laifin nuna halin rashin da'a a gasar Premier a ranar Lahadi.

Vardy an nuna shi a faifan bidiyo yana mayar wa da alkalin wasa Jon Moss kalamai bayan da ya ba shi jan kati a fafatawar.

Leicester ce ta karbi bakuncin West Ham a gasar Premier wasan mako na 34 da suka tashi 2-2 a filin wasa na King Power.

Hukumar ta kuma tuhumi Leicester da kasa tsawatar wa 'yan wasanta, bayan da West Ham ta samu bugun fenariti saura minti bakwai a tashi daga karawar.

An bai wa Vardy da kuma kungiyarsa Leicester daga nan zuwa ranar Alhamis domin su kare kansu daga zargin da ake yi musu.