Juventus na daf da lashe kofin Serie A

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Juventus na shirin lashe kofin Serie A karo na biyar a jere

Juventus na daf da lashe kofin Serie na bana kuma na biyar a jere, bayan da ta doke Palermo da ci 4-0 a ranar Lahadi.

Juventus din ta doke Palermo ne a wasan mako na 33 da suka fafata, kuma Khedira da Pogba da Cuadrado da kuma Padoin ne suka ci mata kwallayen.

Da wannan nasarar da Juve din ta samu wadda ke mataki na daya a kan teburin gasar, ta bai wa Napoli tazarar maki tara, kuma saura wasanni biyar a kammala gasar bana.

Juventus din za ta iya lashe kofin shekarar nan idan ta samu nasara a kan Lazio a wasan mako na 34 a ranar Laraba, idan har Napoli ita kuma ba ta ci Bologna ba a ranar Talata.

Juventus ta dauki kofin Serie A sau 31 jumulla, yayin da Milan da Inter kowaccen su ta lashe shi sau 18.