Maki daya ne tsakanin Barca da Madrid

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saura wasanni biyar a kammala gasar La Liga ta bana

Maki daya ne tsakanin Barcelona da Atletico Madrid da kuma Real Madid, bayan da aka kammala wasanin mako na 33 a gasar La Liga a karshen mako.

Barcelona wadda ke mataki na daya a kan teburi tana da maki 76 iri daya da Atletico Madrid wadda ke matsayi na biyu, sai Real Madrid ta uku da maki 75.

A ranar Asabar Real Madrid ta doke Getafe da ci 5-1, ita kuwa Barcelona rashin nasara ta yi a hannun Valencia da ci 2-1 a Nou Camp a ranar Lahadi, Atletico Madrid kuwa ta ci Granada 3-0 da yammacin Lahadin.

Saura wasanni biyar suka rage a kammala La Ligar bana, Deportivo za ta kara da Barcelona, sai Athletic Bilbao da Atletico Madrid da kuma karawa tsakanin Real Madrid da Villarreal a ranar Laraba wasan mako na 34.

Real Madrid tana da kofin La Liga guda 32, Barcelona kuwa tana da shi 23, sai Atletico Madrid wadda ta lashe kofin sau 10.