Kwallaye 240 aka ci a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto npfl Twitter
Image caption An kammala wasan mako na 12 a gasar Firimiyar Nigeria

Bayan da aka buga wasannin mako na 12 a gasar Firimiyar Nigeria, a karshen satin nan an ci kwallaye 240 daga karawa 112 da aka yi a gasar.

Cikin kwallaye 240 da aka zura a ragar, kungiyoyin da suka yi wasanninsu a waje sun ci guda 65.

Dan wasan Niger Tornadoes, Ismai'la Gata, shi ne jagaba a yawan cin kwallaye a gasar ta Firimiya Nigeria, inda ya jefa bakwai a raga.

Wadanda suka ci shida-shida kuwa a gasar sun hada da Anthony Okpotu na Lobi Stars da Chisom Egbuchulam na Rangers da kuma dan wasan El-Kanemi Warriors Mustapha.