Maki 5 ne tsakanin Leicester da Tottenham

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Harry Kane ya ci kwallaye 24 a gasar ta Premier

Tottenham ta doke Stoke City da ci 4-0 a wasan karshen mako na 34 a gasar Premier da suka fafata a ranar Litinin.

Tottenham ta ci kwallayen ne ta hannaun Harry Kane da Ali wadanda kowannensu ya ci biyu a fafatawar.

Da wannan sakamakon saura maki biyar ya rage tsakanin Leicester wadda take mataki na daya a kan teburi da maki 73 da kuma Tottenham mai maki 68 a matsayi na biyu.

Saura wasanni hudu suka rage a kammala gasar Premier bana, kuma Tottenham za ta buga wasan mako na 35 da West Brom ranar Litinin 25 ga watan Afirilu.

Stoke City kuwa tana mataki na tara a kan teburi da maki 47, za kuma ta buga wasanta na gaba ne da Manchester City ranar Asabar a Ettihad.