Bale ba zai buga wasa da Villarreal ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zidane na fatan Bale zai buga wa Madrid wasa ranar Asabar

Gareth Bale, ba zai buga wa Real Madrid wasan gasar La Liga na mako 34 da za ta kara da Villarreal a rabar Laraba ba.

Dan wasan bai buga wa Wales wasannin sada zumunta da ta yi da Ireland ta Arewa da kuma Ukraine ba, sakamakon jinya da yake yi.

Kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane, na fatan dan wasan zai murmure, domin ya buga wa Madrid fafatawar da za ta yi da Rayo Vallecano a ranar Asabar.

Bale ya ci kwallaye 16 a karon farko a gasar La Liga ta bana tun komawarsa Madrid daga Tottenham, yana daga cikin 'yan wasan da suka ci Getafe 5-1 a ranar Asabar.