Za mu kure gudun Leicester — Kane

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Harry Kane ya ce basa jin tsoron kowanne kulob.

Dan wasan Tottenham Harry Kane ya gargadi Leicester City cewa kulob dinsa na dab da yin kan-kan-kan da su bayan sun samu tazarar maki biyar tsakaninsu a Gasar Premier.

Kulob din Tottenham ya kara kaimi wajen kamo Leicester bayan ya doke Stoke City da ci 4-0 a filin wasa na Britannia ranar Litinin.

Kane ya ce, "Ba za mu fita daga gasar ba. Idan muka ci gaba da jajircewa, babu kulob din da zai doke mu."

Dan wasan mai shekara 22 ya zura kwallonsa ta 24 a gasar Premier ta bana.

Kane ya kara da cewa za su iya lashe kofin Premier ganin cewa wasa hudu suka rage musu a gasar ta Premier.