Newcastle da Man City sun tashi wasa 1-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyoyin biyu sun raba maki guda-guda a tsakaninsu

Newcastle United ta tashi wasa kunnen doki da Manchester City a kwantan gasar Premier da suka kara a ranar Talata a St James Park.

Manchester City ce ta fara cin kwallo ta hannun Aguero kuma ta 21 da ya ci a gasar bana, sannan ta 100 da ya ci a gasar Premier tun komawarsa kulob din.

Newcastle United ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Anita saura minti 14 a je hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon Manchester City tana mataki na uku a kan teburin gasar da maki 61, ita kuwa Newcastle tana matsayi na 19 da maki 29.

City za ta karbi bakuncin Stoke City a wasan mako na 35 a ranar Asabar a Ettihad, a kuma ranar ce Newcastle za ta ziyarci Liverpool a Anfield.