Liverpool za ta fuskanci hukuncin UEFA

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption A ranar 19 ga watan Mayu kwamitin ladabtarwa zai yi zamansa

Liverpool za ta fusakanci hukunci daga hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA, kan jefa abubuwa masu tartsatsin wuta a lokacin wasa.

Za a hutunta Liverpool din ne sakamakon jefa abubuwa masu tartsatsin wuta cikin fili a karawar da ta yi da Borussia Dortmund a gasar Europa.

Tun farko kungiyar na jiran hukuncin da UEFA za ta yanke kan aikata irin wannan laifin da ta da hatsaniya da magoya bayanta suka yi a farko-farkon fara gasar ta Europa.

Liverpool ta kai wasan daf da karshe bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 5-4 a karawa biyu da suka yi.

Kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafa ta Turai zai yi zamansa ne a ranar 19 ga watan Mayu domin daukar matakai kan Liverpool din.