Barca ta zazzaga wa Deportivo kwallaye 8-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona tana nan a matakinta na daya a kan teburi

Deportivo La Coruna ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 8-0 a gasar La Liga wasan mako na 34 da suka kara a ranar Laraba.

Luis Suarez ya ci kwallaye hudu a wasan, sai Lionel Messi da Ivan Rakitic da Marc Bartra da kuma Neymar Da Silva da kowannensu ya ci dai-dai.

Da wannan sakamakon Barcelona tana nan a matakinta na daya a kan teburin La Liga da maki 79.

Barcelona za ta buga wasan mako na 35 a gasar ta La Liga da Sporting Gijon a ranar Asabar a Camp Nou.