Neuer ya sabunta kwantaraginsa a Munich

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manuel Neuer tare da fitaccen dan wasa Lionel Messi.

Golan Bayern Munich, Manuel Neuer, ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyar a kulob din.

Kafin ya sanya hannu a sabon kwantaragin, kwantaraginsa na baya zai kare ne a shekarar 2019, amma zai bi sahun wasu 'yan wasan kulob din, irin su Jerome Boateng da Thomas Muller da David Alaba da Javi Martinez wajen ci gaba da zama a kulob din har shekarar 2021.

Tunda ya shiga Bayern din daga Schalke, dan asalin Jamus din mai shekaru 30, ya yi nasarar lashe Kofuna uku na Bundesliga da Kofi biyu a wasannin Jamus, da kuma gasar zakarun Turai.

Tawagar Pep Guardiola na kan hanyar lashe Kofi a karo na uku.

Bayern Munich ta lallasa Werder Bremen da ci 2-0 a wasan dab da na karshe na cin Kofin Jamus ranar Talata, kuma za su buga wasan karshe da kulob din da ya yi nasara tsakanin Hertha Berlin da Borussia Dortmund ranar Laraba.

Wannan ne wasa na karshe da Guardiola zai jagoranci kulob din kafin ya koma Manchester City, inda tsohon shugaban Chelsea Carlo Ancelotti zai maye gurbinsa.