Galadima zai yi sulhu kan rikicin NFF

Image caption Ibrahim Galadima zai jagoranci kwamitin sulhu na NFF

An zabi tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Nigeria, Ibrahim Galadima ya jagoranci kwamitin sulhu domin shawo kan matsaloli da suka adddabi hukumar.

Ministan wasanni na Najeriya, Solomon Dalung ya bukaci kwamitin ya samar da zaman lafiya a hukumar ta NFF.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban wani bangare na hukumar, Chris Giwa ya ci gaba da kalubalantar shugabancin Amaju a matsayin shugaban NFF.

Galadima ne ya shugabanci NFF tsakanin shekarar 2002 da shekarar 2006.

A baya bayan nan ne wata kotun yanki ta yanke hukuncin cewa a bai wa Giwa shugabancin hukumar kuma a kori Amaju Pinnick wanda hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta dauka a matsayin shugaba.