Giroud na kamfar cin kwallaye a Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwallaye 12 Olivier Giroud ya ci wa Arsenal a gasar Premier bana

Dan wasan Arsenal, Olivier Giroud, na kamfar ci wa kungiyar kwallaye a gasar Premier ta bana.

Rabon da Giroud wanda ya ci wa Arsenal kwallaye 12 jumulla a bana ya ci kwallo, tun biyun da ya zura a ragar Liverpool a ranar 13 ga watan Janairu a wasan Premier.

Dan wasan ya fara ci wa Gunners kwallo ne a bana a karawar da Arsenal ta doke Crystal Palace 2-1 a gasar Premier ranar 16 ga watan Agusta.

Sai dai kuma ya ci guda biyu a karawar da Arsenal ta ci Hull City 4-0 a gasar FA a ranar 8 ga watan Maris.

Giroud ya yi wa Arsenal wasanni 53 a bana, ya kuma ci kwallaye 22, an ba shi katin gargadi sau bakwai da kuma jan kati daya a wasan da Arsenal ta yi da Dinamo Zagreb a gasar cin kofin zakarun Turai.