Boksin: Anthony Joshua zai kare kambunsa

Hakkin mallakar hoto Getty images
Image caption Ba a bayyana wanda zai kara da Anthony Joshuan ba kawo yanzu

Zakaran damben boksin na duniya mai riƙe da kambun IBF Anthony Joshua, ya ce zai yi damben kare kambunsa na farko a dandalin O2 Arena da ke Landan ranar 25 ga watan Yuni.

Joshua mai shekara 26, ya bayyana labarin ne a wani hoton bidiyo da ya sa a shafinsa na Twitter, inda ya ce, ''ina son na yi damben ne a wata rana mafi kusa saboda ina jin ƙarfin jikina.''

Joshua, wanda shi ne zakaran damben ajin manyan masu nauyi na gasar Olympics ta 2012, ya yi nasarar cin kambun hukumar ta IBF ne bayan da ya doke mai riƙe da kambun Ba'amurke Charles Martin, a turmi na biyu.

Ya samu nasarar ne a farkon watan nan a damben da ya yi na ƙwararru na 16, waɗanda dukkanninsu kuma ya gwabje abokan karawar tasa da dukan kawo wuƙa.

Eja ɗin ɗan damben Eddie Harn, a da ya sanar da cewa zakaran zai yi dambensa na gaba ne ranar tara ga watan Yuli a filin Wembley.

Amma aka sauya hakan bayan da zakaran damben boksin na ajin masu nauyi mai riƙe da kambun WBA da IBO da WBO Tyson Fury, ya sanar da cewa zai yi karon battarsa na biyu da Wladimir Klitschko a wannan rana a Manchester.