Kayen da muka sha ya bani kunya — Martinez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Martinez ya ce sun yi abin kunya.

Kociyan Everton Roberto Martinez ya bayyana doke sun da Liverpool ya yi da ci 4-0 a matsayin babban abin kunyar da ya gamu da shi a rayuwarsa.

Divock Origi, Mamadou Sakho, Daniel Sturridge da kuma Philippe Coutinho suka zura kwallayen.

An kori dan wasan Everton Ramiro Funes Mori daga wasan minti biyar bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Martinez, wanda ke shan matsin lamba bayan da ya yi nasara a wasanni uku cikin goma, ya ce wasan da suka yi ya ba shi kunya.

Ya ce, "Babu abin da ya fi wannan takaici. Komai ya tabarbare mana".

Rabon Everton da samun nasara a filin wasan Anfield tun a shekarar 1999.