Hodgson: Bai kamata a kori Vardy ba

Image caption ''Ina ganin Vardy ya yi rashin sa'a ne kawai''

Kociyan Ingila Roy Hodgson ya ce bai kamata alƙalin wasa ya kori ɗan wasan Leicester City Jamie Vardy ba a kan cewa ya faɗi da gangan domin neman fanareti a wasansu da West Ham.

Kociyan na Ingila ya ce, alƙalin wasa Jon Moss, ya yi kuskuren fahinta ne, domin shi a ganinsa dan wasan ba da gangan ya faɗi ba kuma ba kayar da shi aka yi ba a wasan na ranar Lahadi.

Hodgson ya ce, ɗan wasan ya fadi ne saboda a yadda yake gudu a wannan lokaci abu ne mai wuya daman a ce bai faɗi ba.

An haramta wa Vardy mai shekara 29 wanda ya buga wa Ingila wasa sau shida a karkashin Roy Hodgson, buga wasa daya, amma kuma ana ganin za a ƙara masa hukuncin saboda rashin ɗa'a da ya nuna wa alƙalin wasa.

Leicester ta ɗaya a teburin Premier da maki 73 ta tashi 2-2 da West Ham ta shida da maki 56 a wasan na ranar Lahadi.