Najeriya za ta yi wasa da kociyan riƙo

Image caption Bayan murabus din Oliseh Najeriya ta ba Samson Siasia mukamin kociyan riko

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta ce mataimakin kociyan ƙasar shi ne zai jagoranci wasan sada zumunta da ƙasar za ta yi da Mali da Luxembourg a wata mai zuwa.

A ranar 27 ga watan Maris ne Najeriyar wadda ba ta da kociya tun bayan da Sunday Oliseh ya ajiye aiki bisa abin da ya ce rashin biyansa albashi da saba yarjejeniyar kwantiraginsa, za ta kara da takwararta ta Afrika ta Yamma (Mali) a Paris.

Bayan nan ne kuma ƙungiyar ta Super Eagles za ta kara da 'yar ƙaramar ƙasar Turai, Luxembourg ranar daya ga watan Yuni.

An tsayar da shawarar sa mataimakin kociyan ya jagoranci Najeriyar a wasannnin ne a wani taro da hukumar ƙwallon ƙasar NFF ta yi a Abuja, inda kuma aka zartar da cewa zai yi aikin ne bisa kulawar tsohon kociyan ƙasar Shuaibu Amodu.

An nemi Shuaibu Amodu ya karbi aikin kociyan riƙon ƙwarya na ƙasar amma ya ƙi, yana mai ba da dalilai na rashin ƙoshin lafiya.

Ana sa ran nada tartibin kociyan ƙasar kafin wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniyaa na 2018.

Hukumar NFF ta ce takarar muƙamin kociyan na Najeriya dama ce ga kociyoyin cikin gida da kuma na waje.

Ana ganin samun damar zuwa gasar ta kofin duniya wadda za a yi a Rasha abu ne mai wuya ga Najeriyar, bayan ta kasa samun damar zuwa gasar kofin Afrika biyu a jere, abin da ya jawo rudani a ƙasar mai matuƙar sha'awar ƙwallon ƙafa.