Suarez daidai yake da Harry Kane da Jamie Vardy gaba daya

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Wasan Deportivo na daga wanda Suarez ya fi kokari a tarihinsa

Luis Suarez ya kai matsayin gwanayen 'yan wasan Ingila biyu na yanzu Harry Kane da Jamie Vardy gaba ɗaya idan aka kwatanta su.

Tsohon ɗan wasan na Liverpool ya ci ƙwallaye 49 a bana, wanda hakan ya zo daidai da yawan ƙwallayen da 'yan wasan biyu na Ingila suka ci gaba ɗayansu.

Sai dai ɗan wasan na Barcelona yana da sauran tafiya kafin ya zarta tarihin da Messi ya kafa na cin ƙwallaye 73 a kakar 2011-12.

Ɗan wasan na Uruguay ya ci Ƙwallaye hudu ya kuma taimaka aka ci uku a wasan da Barcelona ta Ƙara azamar daukar La Liga, inda ta doke Deportiva La Coruna 8-0 ranar Laraba.

Ƙwallansa ta 30 a gasar ta La Liga ita ce ta zama ta 49 da ya ci a dukkanin gasanni a bana, abin da ya zo daidai da bajintar da ya yi a Ajax a kakar 2009-10.