Chelsea ta ci Bournemouth 3-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na tara a kan teburin Premier

Bournemouth ta yi rashin nasara a hannun Chelsea har gida da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na 35 da suka fafata a ranar Asabar.

Pedro ne ya fara ci wa Chelsea kwallo a minti na biyar da fara tamaula, Hazard ne ya kara ta biyu kuma Willian ya ci ta uku.

Bournemouth ta zura kwallo ne a ragar Chelsea ta hannun dan wasanta Elpick saura minti tara a je hutun rabin lokaci.

Chelsea wadda za ta buga wasan mako na 36 da Sunderland ta hada maki 47 a mataki na tara a kan teburin Premier.