Liverpool da Newcastle sun buga 2-2

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Newcastle tana mataki na 19 a kan teburin Premier

Liverpool ta tashi wasa 2-2 da Newcatle United a wasan mako na 35 a gasar Premier da suka kara ranar Asabar a Anfield.

Liverpool ta ci kwallayenta ne ta hannun Daniel Sturridge da Adam Lallana.

Bayan da aka dawo ne daga hutun rabin lokaci Newcastle ta farke kwallayen da aka zura mata ta hannun Papiss Cisse da kuma Jack Colback.

Liverpool za ta buga wasan gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa da Villarreal, sannan ta buga da Swansea a gasar Premier wasan mako na 36.

Newcastle United kuwa za ta karbi bakuncin Crystal Palace ne a St James Park a gasar ta Premier.