Ya kamata mu lashe wasanninmu - Enrique

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona ce ke mataki na daya a kan teburin La Liga

Kociyan Barcelona, Luis Enrique, ya ce suna da bukatar lashe sauran wasannin La Liga da suka rage, domin lashe kofin bana.

Sauran wasanni uku suka rage a kammala La Ligar shekarar nan, kuma Barcelona za ta karbi bakuncin Sporting Gijon a ranar Asabar.

Barca mai rike da kofin bara, tana mataki na daya a kan teburi da maki 79, ita ma Atletico Madrid mai matsayi na biyu a kan teburin da maki 79 za ta kara ne da Malaga a ranar Asabar.

Real Madrid kuwa mai mataki na uku a kan teburin da maki 78 za ta ziyarci Rayo Vallecano a wasan mako na 35.

A ranar Laraba ne Barcelona ta doke Depotivo La Coruna da ci 8-0 a gasar ta La Liga wasan mako na 34 da suka buga.