Man City ta doke Stoke City da ci 4-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City tana mataki na uku a kan teburi kafin Arsenal ta yi wasa ranar Lahadi

Manchester City ta doke Stoke City da ci 4-0 a gasar cin kofin Premier wasan mako na 35 da suka kara a Ettihad a ranar Asabar.

Fernando ne ya ci wa City kwallon farko, sai Sergio Aguero ya ci ta biyu a bugun fenariti, sannan kuma Kelechi Iheanacho ya ci biyu a wasan.

An ci Stoke City kwallaye hudu a wasanni uku a jere a gasar ta Premier kenan.

A ranar Talata Manchester City za ta fafata da Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da karshe.