Real Madrid ta doke Rayo Vallecano 3-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid za ta fafata da Manchester City a gasar zakarun Turai

Rayo Vallecano ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid da ci 3-2 a gasar La Liga wasan mako na 35 da suka kara a ranar Asabar.

Vallecano ce ta fara cin Madrid kwallo a minti na bakwai da fara tamauala ta hannun Embarba sai Fedor Flores ya ci ta biyu minti bakwai tsakani.

Saura minti 10 a je hutun rabin lokaci ne Garth Bale ya ci wa Madrid kwallo, kuma Vázquez Iglesias ya ci mata ta biyu, kuma Bale din ya kara ta uku kuma ta biyu da ya ci a wasan

Saura wasanni uku suka rage a kammala gasar La Ligar bana, kuma Real Madid tana da maki 81 a gasar.

Madrid wadda za ta fafata da Manchester City a wasan daf da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, za kuma ta ziyarci Real Sociedad a wasan mako na 36 a gasar La Liga.