Dan Aminu da Jimama sun yi canjaras a dambe

Image caption Turmi biyu suka taka babu wanda ya je kasa a karawar

Dan Aminu da Shagon Jimama sun tashi wasan damben gargajiya babu wanda ya je kasa a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria ranar Lahadi da safe.

Dan Aminu Langa-Langa daga Arewa ne ya bukaci Shagon Jimama daga Kudu su saka zare a tsakaninsu, kuma hakan suka yi turmi biyu aka raba su da wasan bai yi kisa ba.

A ranar an fara damben da Sanin Kawo daga Arewa ya buge Bokan Dan Sama'ila a turmin farko, suna takawa Sanin Kawo ya laftawa Bokan Dan Sama'ila kafa a baki ya zubar da shi kasa.

Damben da aka yi tsakanin Dan Kanawa daga Kudu da Nura Shagon Dogon Sani daga Arewa turmi biyu suka taka babu kisa alkalin wasa Tirabula ya raba su.

Gumurzun da aka yi tsakanin Nokiyar Dogon Sani daga Arewa da Bahagon Dogon Auta dag Kudu turmi biyu suka yi babu kisa a karawar.

Damben karshe da aka yi tsakanin Dan Aliyu daga Arewa da Shagon Wale daga Kudu turmi biyun suka fafata, kuma babu kisa aka raba su.