Ba ma son Tottenham ta lashe Premier - Hazard

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea mai rike da kofin Premier na bara tana mataki na tara a gasar bana

Eden Hazard ya ce shi da abokan wasansa na Chelsea ba sa kaunar Tottenham ta lashe kofin Premier na bana.

Tottenham tana mataki na biyu a kan teburin Premier, inda Leicester wadda ke matsayi na daya ta ba ta tazarar maki biyar, kuma saura wasanni uku a kammala gasar bana.

Chelsea za ta karbi bakuncin Tottenham a ranar 2 ga watan Mayu, sannan ta buga wasan karshe da Leicester ranar 15 ga watan Mayu.

Hazard ya shaidawa BBC cewar Chelsea da 'yan wasa da magoya bayanta ba sa son Tottenham ta lashe kofin Premier kakar bana.

Dan wasan ya kara da cewa suna fatan Leicester ce za ta dauki kofin domin ta cancanta.