Pillars ta doke Shooting Stars 6-0

Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption A karon farko a gasar Firimiyar bana an ci kwallaye shida a wasa daya

Kano Pillars ta doke Shooting Stars da ci 6-0 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 13 da suka kara ranar Lahadi.

Ifeanyi Matthew ne ya fara cin kwallon, sai Emmanuel Edmund wanda ya ci uku rigis a wasan.

Daf da za a tashi daga karawar Adamu Mohammed ya ci ta biyar kuma Nafiu Ibrahim ya zura ta shida a fafatawar.

Ga sauran sakamakon wasannin mako na 13 da aka yi a ranar Lahadi:
  • Heartland 1-0 Sunshine Stars
  • Kano Pillars 6-0 Shooting Stars
  • Plateau Utd 2-1 Rivers Utd
  • Wolves 2-0 Giwa FC
  • Wikki 3-0 Ifeanyiubah
  • Abia Warriors 3-1 MFM
  • Lobi 1-0 Tornadoes
  • Akwa United 0-1 Enyimba