Sunderland da Arsenal sun tashi wasa canjaras

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunderland na mataki na 17, Arsenal na matsayi na hudu a teburin Premier

Sunderland da Arsenal sun tashi wasa canjaras babu ci a wasan Premier gasar mako na 35 da suka kara a ranar Lahadi.

Da wannan sakamakon kungiyoyin biyu sun sami maki daya-daya a tsakaninsu, kuma saura wasanni uku suka rage a kammala gasar bana.

Arsenal tana mataki na hudu a teburi da maki 64, yayin da Sunderland ta koma matsayi na 17 da maki 31.

Sauran wasanni uku da Arsenal za ta buga a gaba sun hada da karawar da za ta karbi bakuncin Norwich da wanda za ta ziyarci Manchester City ta kuma rufe wasan karshe da Aston Villa a Emirates.

Sunderland kuwa za ta ziyarci Stoke City ne, sannan ta karbi bakuncin Chelsea da Everton, ta kuma rufe wasan karshe a gidan Watford.